ummul khairi hausa books
HAUSA LOVE STORIES

ummul khairi kashi na uku

Share

khaireeya kashi na uku.

 a hanyarsu ta zuwa kauye,yayin da tanko driver ke ta paman tsalla gudu ,tamkar zai tashi sama shi ko saif sai faman chatting yake abunsa ,inda hajiya na’ima da alhaji nasir ke hiran su irin ta masoya,..hajiya na’ima tace da tanko driver kai tanko kare gudun nan mana tayi yawa sai kace zamu tashi sama..tanko driver ai hajja ju bani ke gudun ba motar ce keda bala’in gudu..alhaji nasir ”oho ! halan motar itake tuka kanta”tanko oga in na tuno lokacin kuruciya ,tanko mai kwana a parenti ,yayi wata duka wa sitirin motar wanda yasa su duk suka razana ,nan fa kowa yasaka mai na mujiya …nayi tuki a legas ,abuja na nayi tun daga mile 2 inna pinciki motar sai oshodi…saif dake gefe bai tamka ba ,,,yace dashi” aiko karika fimcikar ,motar a hankali idan bahaka ba wataran zakaji ka kiyama…

 

sun iso kauye lafiya mutum kauye suka tarbe su hannu bibbiyu,anan tanko yasami gu yapaka motar ,kowa yasan gida irin ta kauye ,awni kauyen samun gida dakeda get yana da matukar wahala ,saif ya sunkuyu jakarsa ya nausa cikin farfajiyar gida yayin da wasu almajirai uku ke taya tanko sauke kaya dake a bud din motar ..bayan yaran almajiran sun ida kwashe kayar saif yazaro 200 yaba wa kowannensu ,suka amsa sukayi godiya …adai dai nan kawu jamilu ya iso daga gonarsa bisa kansa ciyayi yayo wa dabbobinsa ….kawu jamilu”la! yadan dakata nawasu sakwanni ,wannan ba motar ‘yaya nasir bace? ya jeho wakansa wannan tambayar ,wancan dake tsaye ai tanko ne abokina ,tam bari dai nakarasa nagani…

isowa gunsu keda wuya ,tanko? aiko nan tanko yadago kai yaga wanda ke kwala mai kira yasani sarai wanda zai mai irin wannan kiran dan haka ma ya basar dashi…jamilu yanzu tanko kanaji ina ta kiranka kayi burus dani? tanko”ta ai gani nayi ka tahomin babu ko ‘yar sallam,ehye? lallai ma tanko ,ni zaka gwadawa sallama ehye wato kai gaka dan birni…nizaka rainawa hankali,duk dube ka kabi ka canza kuna can kuna karin kumallo da biredi da kwai ,ni anbarni nan kauye ina fama da dumame,alqur’an bazata yiwu ba,wannan karan dani da a tafi birnin nan..yauwa …tanko ya karewa aminin nasa kallo ai tanan kuma zaka bullo,shiko jamilu yamasa wata irin kallo….

irin kallon tara saura kwatan nan,alhaji ubale tare da dan uwansa alhaji nasir zaune cikin falonsa ,alhaji ubale yace nasiru daman dalilin wannan kiran ta gaggawa itace na yanke shawarar hada saifu aure da ‘yar uwarsa ummul khairi,domin kuwa naga dacewar hakan .alhaji ubale yayi shiru nadan wasu seconni sannan yacigaba da cewa kayi hakuri nasiru nayanke shawara batare da na nemi amincewarka ba…”alhaji nasir aibabu komai yaya,ni abin dakayi aikayimin daidai,shi saifullan da ita ummul khairan aiduk ‘ya’ya suke a wajen ka…rokon mu Allah ya tabbatar mana da alkhairin dake cikin wannan lamari..

atare suka furta amin ,toyaya kagama ashe ma bamu gaisa ba…toya mutun gidan ,duk k muna lafiya nasiru,ai yaya danaga kira na zace jamilu yasami wacce yakeso ne ,tabdi jan jamilun ?ai shiriritarsa tayi yawa ,aikuma yana kokari a gona,kaga wannan fadamar taka ?kacokan dinta yanzu shi nabarwa yana nomewa.wannan daka saya gun mati itama nabar masa,..hmnmm! abin yayi wa alhaji nasir dadi…hajiya na;ima zaune  dasu kuluwa,yayin da sarutu ke tsine duwatsu cikin local rice din dake a saman tire ga dukkan alamu yau gidan nasu shinkafa za aci…hajiya na’ima macen kwarai mutumiyar arziki,mace mai hakuri tsapta sam babu ruwanta da shiga sapgar da batataba,hakan yasa su matan wan mijin nata ke girmamata ,hattta mutum kauyen saboda batada hannun ‘yan dambe,inanufin hannuta a bude yake..saratu,sai wata kitsi-tsina takewa kuluwa ,abun yayi matukar bawa na’ima mamaki to wadannan kuma yaushe suka shirya? nan pa saratu ta care da guda aiyirii riii,kuluwa hajjaju uwar ango kunpasha hanya,aiko mun gama duk wata shiri da za ayi ,ita ko hajiya na’ima abin kara kulal da ita yayi ,dan bata sam ma abin da suke cewa ba.ta ce dasu .shirin me ?idan na fahimta aure jamilu zai yi…ehye! saratu da kuluwa sukayo tafi alokaci guda…

 

nan saif yayo sallama yashigo inda iyayen nasa suke ”yayo musu cikkakiyar sallama assalma alaikum waalakas salam ango mijin amarya,saif shima abin ta kulal dashi ainun amarya kuma?,wacce amaryan ,waye zaiyi auren?..irein wannan tambayoyi haka ajere wannan kakeso afara ansa ma ,shiko na mujiya ma ya zuba musu,saratu yan hajiya sokike ke da danki ki cemana bakusan auren saif za’ayi ba da wannan yarinyar ummul-khairi?hajiya na’ima ko girgiza musu kai tayi alamun sam batasan da zancen ba..saif yace da su …no no please matan kawu dan allah karkucemin da waccan mayyan za a hadani aure…nooooh yadafe kansa…no dan allah..

bayan alhaji ubale ya kira wo saif da ummul-khairi barinsa.

duk suna a zaune kasa yayin da alhaji ubale ke zaune bisa kujera ,ina mai farawa da baku hakuri ,na hada aurenku batare da amincewarku ba,dalilina nayin hakan kuma shine ni inaga naga isa daku,ni mai son ganin farin cikinku ne ,kuma inaso kusani ita zaman aure zama ne na ibada bawai ta cimma wata manufa ba ta daban,idan kaji kakiji ,kekuma kika gani kuma kika ki gani,zakuyi zaman aure irin wacce ba ataba irinta ba.saif da ummul-khairi ko ina da tabbacin cewa bawani jinsa suke ba dan kowa da abin dake aiyanawa cikin zuciyarsa ,sai kuma aikin aikawa juna harara suke…can suka jiyo shin koda mai magana ?duk suka girgiza kai …alhaji ubale kai saifu kaine babba kuriki juna amana,kuma kuyi kokakari gurin solving din matsalolinku a tsakaninku..tashi kufita…allah yayi muku albarka..

fitan su daga dakin kawun nasu kedawuya ,suka nausa inda motarsu take ,yayin da saif ke zaune saman booth din mota ,sai aikin latse latse yakeyi cikin wayarsa ,itako ummul khairi a tsaye kuma cikin shiga ta mutan kauye,shiru sai kace an aiki bawa garinsu,sunfi mintuna goma a haka babu wanda ya cewa kowa komai,ummul khairi dataga shirun tayi yawa sai ta dan yi gyaran murya..saif ya hada rai  yace maiya da wani abu? daman shiru-shiru din nan taki ta munafurci ne ….yasake hada rai tukunnama maye matakin karatunki?….nan ta sunkai da kai kas tace….!

 

 

kash zamu cigaba…kucigaba da bibiyar shafinmu….kamu karkumanta kusuburbuda mana comments,,,tare da yin liking din pagin mu ta facebook #nassblog

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *