LABARAN DUNIYA

siffofin mutanen kirki

Share

yiwa iyaye addu’a yanadaya daga siffofin mutanen kirki,an tambayi daya daga cikin magabata wannan tambaya daya daga cikin dalibansa ya ce dashi ” shin mallam ina cikin mutane salihai? mutumin kirki?.” sai ya amsa da cewa ”idan har kana yiwa iyayenka addu’a ,to hakika kana cikin mutanen kirki ,salihan bayi  na kwarai ,saboda hadisin da manzon allah tsira da amincin allah sutabbata a gareshi yana cewa .”idan dan adam ya mutu dukkan ayyukansa sun kare ,ma’ana ladan ayyukansa ta daina karuwa ko gudana ,sai abubuwa uku

-sadaka mai gudana: kamar wanda ya gina masallaci ko wata rijiya al’umma suna ampanuwa.

-ko wata ilimi daya koyar: anan dai malaman islamiya da tsangayuyin koyar da addini sun tahi da lada..

-kowani yaro salihi dazai rika yimasa addu.a…   sahihul jam’i..

sai annabi yatabbatar mana anan cewa yana daya daga cikin babban alamar salihin mutum yakasance yana yiwa mahaifansa addu.a a akowane lokaci,idan kuma bakayi musu ba ,to ga  dukkan alamu kai ba mutumin kirki bane ,iya yadda kamance da yiwa mahaifanka addu,a iya yadda kazam mtumin banza….Allah kabamu daman yiwa iyayen mu addu,a..amin

dan haka masu karutu ina kira da muyawaita fadar ”ya ubangijina ! kayi musu rahama ,kamar yadda sukayi renona ina karami”ita wannnan addu,ar ta kunshi abubuwa biyu da akeso muyawaita yiwa iyayenmu addu,a

na farko nema musu gafara gurin ubangijin talikai,na biyu nema musu aljanna da nema musu tsira  da tsri daga wuta da azabar qabari,..ya Allah kayi rahama da jinkai da gafara ga mahaifanmu damu baki daya.

 

babi na biyu.

su waye mafi soyuwar mutane gurin Allah,abdullahi ibn umar (ra) yana cewa lallai manzan allah(s.,a.w) yana cewa mafi soyuwar mutane a gun allah sune wanda sukafi anfanar da mutane ,yana cewa ,wannan hadisin lallai yanuna cewa lalai dukkan wanda ya taimaki wani ko ya taimakawa mutane cikin yin ayyukan biyayya ga allah da manzoinsa to yana da irin ladar aiyukan da suka aikata, idan ka taimakawa dalibi kasaya masa littafin karatu ko kabashi wajan zama dan yin karatu,ko kana ciyar dashi ko dukkan wani taimako dazai bashi daman yin karatunsa ,to kanada ladan dukkan wani abinda ya samu na wannan ilimi ba tare da anrage maka komai na lada ba.

haka zalika inkataimaki mai yin sallah da saukaka masa shan wahala wajen yin alwala  ko gurin yin sallah  ka kyautata wajen yin sallah da jindadi ,ko kabashi tufafin dazaiyi sallah ,to kana da ladar wannan sallah ba tare da an rage komai daga ladar ba.  ka’ida gamammiya dukkan wanda yataimaki wani mutum cikin yin biyayya ga allah da manzonsa koyin wani aiki na alkhairi,yana da irin ladar abin da mutuman ya aikata ba tare da anrage wani abu daga cikin ladarsa ba…allah ya samuda ce..

shin kun sani?  sadaka tana hana zafi da kuncin qabari…ita qabarishine masaukakin farko daga cikin masaukai aranar kiyama idan dan adam ya tsira acikinsa to abinda zai biyo bayansa zai zo masa da sauki ,amma idan ya tabe acikinsa to abinda zai biyo bayansa yafi tabewa da wahala..qabari yana zama dausayi daga dausayin aljanna ,allah yasanya tamu ta zam haka ,amin..ya kare tamu daga zama ramika cikin jahannama …amin…

kar amanta arika bibiyar shafin tamu ta nassblog/hausa news…sannna  asuburbuda mana share,comments da ma likes

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *