ali nuhu da abokan aikinsa
AREWA CELEBRITIES AREWA24

sana’a shida datafi kawo kudi

Share

Akwai aiyuka da dama a Najeriya da suke kawo wa masu yinsu kudi. Yawancin irin wadannan aiyuka suna bukatar basirar mutum, gogewarsa ko kuma ilimin da yake da shi. Idan mutum yana da daya daga cikin wadannan abubuwa uku, zai iya samun daya daga cikin aiyukan da suke kawo kudi ba tare da bata lokaci ba.

1. Nishadi (jaruman fim da mawaka): Sanannen abu ne cewar harkar masana’antun nishadantar wa na kawo kudi a duk fadin duniya. Masu nishadantar wa na samun miliyoyi daga sana’ar nishadantar da jama’a. Ko a nan gida Najeriya, mawaka irinsu Davido, Wizkid, Rarara, Naziru M. Ahmad da sauransu na samun miliyoyin Naira duk lokacin da suka yi taron rera waka don nishadantar da jama’a ko yabon mai mulki, basarake, attajiri ko dan siyasa.
Haka bangaren jaruman fim da masu shirya fina-finan da suka hada da darektoci da furodusoshi ke samun kudi masu nauyin duk lokacin da suka bayyana ko fitar da sabon fim.ali nuhu da abokan aikinsa

Sarkin kannywood ,ali nuhu a tsakiya tare da abokan aikinsa.
2. Likitanci: Duk da wasu na korafin cewar ba a biyan likitoci da kyau a Najeriya, suna daga cikin jerin ma’aikatan da suka fi daukan albashi me tsoka saboda darajar takardar karatunsu da kuma gogewa. Alal misali, kwararren likita a Najeriya zai iya daukan albashin da ya kai N1m duk wata.
Likita

3. Lauya: Ba da zarar mutum ya kammala karatun lauya yake fara samun kudi ba, amma duk da hakan lauyoyin na daga cikin masu samun kudi a Najeriya. Matukar lauya ya kware kuma bashi da tsoro wajen wakilci a kotu, tabbas zai ke samun kudi masu nauyi.
DUBA WANNAN: Kuncin rayuwa: Wani mutum ya banka wa kan sa wuta bayan ya yi korafi da yunwa

4. Tukin jirgin sama: Saboda hatsarin da ke cikinsa, tukin jirgin sama na daga cikin aiyukan dake kawo kudi a fadin duniya. Wata majiya ta ce direbobin jirgi a Najeriya na daukan albashin da ya kai N500,000 zuwa N1m duk wata. Albashin ya sha ban-ban daga kamfani zuwa kamfani.

5. Injiniya: Injiniyoyi, musamman masu aiki da kamfanonin man fetur na samun kudi masu yawa daga aikinsu. Bisa la’akari da bangaren injiniyarin da mutum ya karanta, injiniyoyi na daukan albashin N8m, N10m zuwa N12m duk shekara.

6. Tukin jirgin ruwa: Duk da irin kudin da ke cikin aikin, matukan jirgin ruwa na wuyar samu a Najeriya. Kamar tukin jirgin sama, akwai hatsari a cikin aikin tukin jirgin ruwa.
Tsirarun jami’o’i ne ke koyar da ilimin tukin jirgin ruwa a Najeriya.

7.blogging : aikin jarida ta wucin gadi,dayawa  wasu basa san banbancin dake tsakanin blogging da  freelancing ba,ita blogging kafin ka fara ta kana bukatan yan kudade,kudi da zaka sai fili,suna wanda ake kira hosting and domain,ita ko freelancing kawai registrer zakayi da kampanin su ta freelansa bayan ka cike duk abin da ake bukata ,nan zaka fara tallar duk wani aiki dakake da kwarewa ake,masana sun kiyasta cewa wannan harka ta blogging da freelancing tana kawo kudi da dama..wanda sukayi nasara cikin harkan blogging nan kasa nigeria munada su linda ikeje wanda akalla tana samin naira million 13 duk wata daga google adsence..

 

8.youtube  : babu shakka da dama wasu kawai app ko ince ziyartar youtube kawai suke dan kallon fina_fiani. da yawa wasu kuma basasan cewa harkan youtube tana daya daga cikin abin dake kawo kudi ba a duniya ,duk da cewa kamfanin google ita ke da youtube,inda ake samun kudi da youtube kuwa shine ,bayan kayi register mallakal shafi naka wato (channel) sai ka fara posting din bidiyo ,bayan chanal din tasami mabiya 1000 kuma tasami  awa 4000 ta kallo,kuma akalla ta kai shekara guda …nan chanal din kacika sharuda na samin gurbin youtube monetising…shikenan aka ce daman bayan wuya sai dadi..akalla manya cikin harkan youtube sun tabbatar da suna samun akalla $1 millon duk wata,anan gida nigeria kuma inkukayi duba akwai su broda shagi duk basa da wani aikin yi inbanda aikin posting din bidiyo a youtube..

to abokai kar kumanta dai kuyi mana sharing….mungode….#nassblog /hausa news takuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *