sheik kabir gombe
AREWA24 LABARAN DUNIYA Uncategorized

sahabin daya fada hannun rumuwa.

Share

hijirar ma’aiki s.a.w inda yaraba ganimar yakin hunain.

sheik kabir gombe
sheik kabir gombe tare da ahmad sulaiman

An karbo daga Dan hatim yace rauhu Dan ubadatu yabanu labari yace sa,ad yabamu labari daga kattada yace ” anas Dan malik ya ambata mana daga Abu dalhat Allah ya yarda dasu daga annabi (s.a.w) cewa lallai ” shi ya kasance idan ya kasance idan ,ya samu nasara akan abokan gaba, yakan zauna a farfajiyar gari kamar kwana uku.
Wanda ya raba ganimarsa ta yaki ko abisa hanya komawarsa daga tafiya rafi,u yace mun kasance tare da manzon Allah a lokacin da muka iso zulhulaifa,mun sami taguwa da tumaki,kuma yadaidaita tumaki coma bisa taguwa daya,an karbo daga hudabat Dan Khalid yace ” hamman yabamu labari daga kattada cewa ” lallai Ana’s yabashi labari yace Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yayi umra daga ji,ranata inda yaraba ganimar yakin hunain.

Idan kafiri yasamu ganimar dukiyar musulmi sa,an nan shi musulmi ya iske ta Dan numair yace “ubaidulla yabamu labari daga nafi,u daga Dan umar Allah ya yarda dasu yace ” doki ya taba gudu masa,sai abokin gaba yakamashi ,anan musulmi suka sami nasara akan kafiran .sai akamayar masa a lokacin manzon Allah ,kuma bawansa yataba gudu yafada a hannun rumawa ,lokacin da musulmai suka samu nasara akan su Khalid Dan walid ya mayar masa da bawansa bayan rasuwar manzon Allah.

***
Bayan shekara daya da yin bai,ar farko ga annabi a shekara ta 13 da aiko shi ,mutanen madina sun zo makka aikin hajji ,said suka ce lallai su bazasu bar annabi a makka ba don haka suka hadu dashi a cikin kwanakin tashrik na dare a inda jamrstul akaba take ,shi yasa ake Koran wannan bai,a da bai,atul akaba .yawan mutanen su saba,in da uku ne sittin da biyu daga kabilar khazraj,goma sha daya kuma daga kabilar ausu,sai dai mata biyu ne kawai a cikinsu nusaiba yar ka,ab daga bani najjar da asma,u yar amru daga banu salma.sun fita da dai dai zuwa mutum bibbiyu ne don kada a gane wannan taro nasu dasuka kulla na haduwa a sirce ,annabi (s.a.w) ya iske su atare dashi akwai Dan uwan mahaifinsa Abbas (RA) a lokacin bairiga ya karbi addinin. Musulunci ba,yadai halasta ne Dan ya sa ido da samun amnminci gadan uwansa,Abbas (ra) shiya fara magana yanuna musu lallai fa annabi (s a.w)ya nada izza a cikin mutanensa idan kunsan bazaku cika masa alkawarin dakuka yiba ,to tun yanzu Ku kyale shi.

        A wannan taron ganawa tsakanin Annabi (s.a.w) da wakilan mutanen madina an cimma wasu yarjeneniyo a tsakanin bangarorin biyu ,abubuwan da aka zartar a wannan taro sune:
– kada ayi tarayya da Allah wajen bauta
-kada ayi sata
-kada ayi zina
-banda kashe yaya mata
-banda jefa kalmimin kazafi a tsakanin nuna
– banda sabawa annabi adukkan lamura
– yin biyayya ga umurmin annabi (s.a.w) a cikin sauki da tsanani

***

           hudubar manzon tsira wanda yayi ta ranar tara ga watan zulhijja ,shekara ta goma da hijira a dutsen arfa..

ma’aiki ya fara da cewa

“Ya ku mutane ku bani hankalinku, domin mai Yiwuwa bazan sake kasancewa da ku bayan wannan shekaran ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda basa wannan wuri a yau.

Ya ku mutane kamar yadda kuka riki wannan wata, (na hajji) da wannan rana (ta arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki Ran Musulmi da kuma Dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa, ku maida wa Mutane kayan da suka baku Amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku, ku tuna fa, hakika ALLAH zai yi sakayya akan ayukakanku, ALLAH (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.

Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye Addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka ku guji binshi akan kanana.

Ya ku jamaa hakika kuna da hakki bisa matayenku, amma suma suna da hakki bisa kanku, to hakkin su ne akanku da kuciyar dasu, Kuma ku tufatar dasu akan jin kai. ku bi dasu kyakkyawan biyarwa, ku kuma tausasa musu domin su majibintan al amurran kune, kuma mataimakan ku, Hakki ne akansu da kar su yi abota da duk wanda ba kwa so, kuma su nisanci zina.

Ya ku jama’a kuyi kyakkyawan bauta ga ALLAH (SWT) ku tsaida salloli biyar(5) na farilla, Ku Azumci Watan Ramadan ku Kuma bada zakka. Ku aikata aikin hajji in har kun sami daman yi. KU SANI FA, ko wane musulmi dan uwan musulmi ne. Dukkan ku dai dai kuke. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai ta tsoron ALLAH, da aikata kyawawan ayyukka.

Ku tuna fa(ya ku jama’a) wata rana za ku tsaya gaban ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku, saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da hanya madaidaiciya bayan na kau.

Ya ku jama’a ba wani annabi ko manzo da zai zo bayana kuma babu wani addini da zai zo (bayan addinin musulunci), saboda haka kuyi tunani sosai akan wannan magana dana gaya maku, kuma ku fahimce ta (sosai).

Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); ga (alkur ani) ga kuma (sunnah) ta. In kun bi wannan ba za ku ta ba bata ba. Duk Wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, suma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji magana daga karshe sufi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.

YA ALLAH ka zamo shaida agareni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka.” Yan uwa ku watsa wannan KHUDUBAR ga yan uwa musulmi wanda kamar yau akayi ta!!!

Allah duk wanda ya tura wannan khuduba ya Allah ka sadashi da annabin MuhammadMuhammad (saw) ya Allah kabiya masa dukkan bukatunsa na alkhairi.

SALLAH ITACE MAFI ALKHAIRI DAGA BACCI!!!

Me nene yasa Sallah tafi Alkhairi daga Bacci???

Amsa:

1.Bacci amsawa kiran Zuciyane

Sallakuwa amsawa kiran Ubangiji ne

2.Shi Bacci mutuwane

Sallakuwa Rayuwace

3.Shi Bacci hutune na Gangar jiki

Sallakuwa hutune na Ruhi

4.Shi Bacci da Mumini da Kafiri duk suna yinsa.

Sallakuwa Mumini ne kadai yake yinta

Masu tashi lokacin hudowar Alfijir sun rabauta, Fuskarsu kuma ta haskaka Goshinsu kuma shima yayi haske da kyalli, Lokacinsu kuma yayi Albarka. Idan kana cikinsu to kagodewa Allah.s.w.t. daya fifitaka idan kuma baka cikinsu to Karoqi Allah.s.w.t yasakaka acikinsu.

Menene yafi Alfijir kyaune?

Farillarsa(Sallar Asuba) zata sakaka acikin kulawar Ubangiji da kariyarsa,

Sunnarsa (Raka’ataylfajri) itace tafi Duniya da abinda yake cikinta

Sallarsa (kamar yadda Malaman tafsiri suka fassara wannan aya ta 78 Suratul – Isra’i وقرآن الفجر ana nufin Sallar Asubahi)

Ita Sallar Asubahi Mala’iku masu duty n safe da masu dutu n dare duka suna halartota.(Domin alokacin suke handing over na duty n su acikin wannan Duniya tamu)

Yakai Dan’uwa Mai girma kasani cewa : Duk wanda yarayu akan wani aiki to akansa zai mutu, Wanda kuma yamutu akan wani aiki to akansa za’a tashe shi

Idan kakaranta wannan Saqo kuma kayi aiki dashi to kasami Ladan aikin ka idan kuma katurawa wasu suma sukayi aiki dashi to Ladanka zai nunku awuri Allah.s.w.t In Allah.s.w.t yaso.

Kada kaboye Ilimi, Kabayyana shi zaka sami Kyakkyawan Sakamako

Kuyi Murna yaku masu Sallar Asubahi acikin Lokacin ta kuma acikin Jam’i.abokai munyi rashin malimi mai tawali’u https://www.nassblog.com/blog/ina-kafito-daawa-sheik-jafar-adam/

 

jumu,at mufeedat….dan allah karkumanta kuyi share dan ‘yan uwa sukaru …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *