marigayi sheik jafar da 'ya'yansa
AREWA24 LABARAN DUNIYA

ina kafito da’awa sheik jafar adam…

Share

kadan gada tarihin sheik jafar mahmud adam kano rahimahullah..
” lallai watan wata rana zata zo,zaka ce da abokanka sai da safe sai da safe safiyar da baza ayita da kai ba ” inji sheik jafar mahmud adam kano ,rahimahullah….yanzu shekaru sha uku kenan cur da rasuwan babban shehin malamin musuluncin dan asalin jahar kano …lallai shakka babu wanda ya mutu baiyi sauri ba ,wanda kuma ke raye baiyi jinkiri ba ..shekaru sha uku kenan cur da wadan su la’anan nu ,shashashu ,wadanda suka kwashe shimfidarsu daga rahamar allah ,suka zabi kaskanci ,sukayi wa fitatcen malamin nan sheik jafar adan kano kisan gilla .tare da jimami da alhini…
ranar juma,ar ga watan afrilun 2007 ,wadan su ‘yan bindiga da sanyin asuba suka halalci masallacin da marigayi sheik jafar ke limanci a unguwar dorayi ,birnin jahar kano,suka iske shi yana jagorancin mafificiyar sallahr asuba ,suka dilma masa dalmomi a jikin sa ,malamin wanda ke cikin sujjada ga allah subuhana hu wa ta ala.yayi shahada …wa iya zubllah mallam yasha fadan cewa wasu mutane suna son ganin bayansa ,ansha bogu masa wayar kar ta kwana dan sutambaya koya mutu,bokaye ne ‘yan siyasa ne abokan gaban mallam allah shi yabarwa kansa sani..
babban abin takaicin game da lamarin ,ba wai yanayin mutuwarsa ce ba,babban asarar da aka dibga wa al’umma ,alokacin da malam yara su ,lokaci ne da mutane ke bukatarsa ,mutumin ne mai tsoron allah,tawa li’u mutumin ne daya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen karatu da karantarwa ,fadakarwa ,akara da ankararwa .alokacin da mafi maluman addini suka zama makwa daita shi malam saiya zama daban ,daya tamkar dubu,ya kasance wanda yasan kansa ya rike mutuncin kansa …alokacin da wasu malaman suka siffantu da karkatar da mabiyuansu saboda neman girma da neman abin duniya ,shehin malamin ya kasance kaifi daya .ya dora koyarwarsa bisa turba daya ,bisa hujja mai inganci ta Alqur’ani da hadisi da ijma’in malaman sunna magabata na kwarai.
babu shakka wannan hali ne yabashi daman kasancewa jajir tattace,wanda bayada kyuya ko kasala.akullum yana cikin nazari da bincike,wanda bai fadin wata fatawa face yana da hujja da kwakkwarar madogara ..malami ne da ya kau cewa harkar kungiyanci,idan gaskiya tazo komai dacinta bai shayin fadanta .allah ya jikan malam da rahama alakacin daya fara ganin take taken marigayi shugaban boko haram ,malam mahmud yusuf ,sheik jafar yayi iyaka kokarinsa wajen fadakar dashi ,game da fitinar dayake son kunnowa ga al’ummar nigeria ,shi ko mahammad yusuf yayi burus abinsa yayi kunne uwar shegu da huddubar jafar,sai gashi abin da malam ya hango tazam gaskiya .ayau kungiyar boko haram tazan annoba wa nijeriya,camaroo da yankin chadi,
marigayi sheik jafar ya haifar da sauyi mai girma ga al’umma musamman ma matasa mazan su da matan su,inda suka fahimci tsantsar abin da musulunci ke koyi da koyarwa.ta hanyar wa,azozinsa da karutunsa ,al’umma sunkaru sosai da nagartaccen ilimi kuma ana ciga ba da amfana,kiyasi ta tabbatar da cewa karatunka malam sun fi na duk wani malami karbuwa da saurayo duk da cewa malam baya raye.al’ummar musulmi sun fahimci tsantsar abin daya ake nufi da rayuwa ,sun gane tasirin neman ilimi ,sun fahimci tasirin neman aiki kop sana’a,kamar yadda suka gane illal zaman kashe wando …
karantarwar malam bai bar shugabanni ba ,bai bai masu sarautar gargajiya ba ,haka zalika bai bar ma’aikatan gwamnati ba ,bai bar yan kasuwa ba kamar yadda bai bar talaka ba ,idan mai kudi ko mai mulki ya kaucewa gaskiya ,balo-balo zai fito ya fayyace masa illal haka ,yayi yaki da azzaluman duniya ,ya fayyace fari daga baki,ya sassaita tunanin al’umma da hasken iliminsa ..wata abar bakin ciki shine har izuwa yau din nan yau shekaru sha uku da rasuwar malam ba akama wani ko wasu ba da ke da hannu a kisan mallam
kadan daga cikin tarihin malam …an haifi malam jafar mahmud adam kano ranar 12 ga watan febrairun 1960 a garin daura dake jahar katsina ,yasami gurbin karutun gaba da firamari a 1984 inda ya shiga kolejin harar da malamai ta gwamnati dake gwale (GTC) wanda a yanzu ake kiranta kwalejin koyar da larabci ta gwammati (GAC) gwale .ya kammala a 1988 daga nan ya sami gurbin ci gaba da karatu a jami’ar musulunci ta madina a kasar saudiya ,malam yayi karatunsa a can harna tsawon shekaru hudu,inda ya kammala a 1993.malam jafar ya kasan ce ina kafito nazari ,ina zaka nazari ,ina zaka da’awa kocokan din rayuwarsa takasance hidima wa addinin musulunci.muna rokon allah daya kikansa da rahamaj,ya amshi shahadarsa ,yaci gaba da raya ayyukansa a fadin duniya ,allah yayi masa sakayyar zaluncin da aka shuka masa …muna rokon allah da ya tada mana da magajinsa ,wanda zai cigaba da haskaka addininka ga al’umma …malam jafat muna tuna ka muna yi maka addu’a a kullum…allah ya jikanka…

marigayi sheik jafar da 'ya'yansa
sheik jafar mahmud adam da ‘ya’yansa

  MACE !

antambaye wani mai hikima dan gane da mace sai yabada amsa ;idan mace ma’abociyar addini ce to tana da daraja daya =1 ,idan ta zama mai kyau sai akara sipili akai ta zama tana da =10,idan tazama mai dukiya sai akara mata sipili yazama =100 ,idan tazama mai nasaba sai akara mata sipili ta zama tana da =1000….

amma idan ta rasa guda dayan farko wato addini sai acire 1 sai yazama ba abin daya ragu sai sipili=000,dan haka bata da komai na kima da daraja ta rasa duk wani abu da zai mata ado da gata a duniya da lahira ,yake ‘yar uwa kiyi ado da addini da ‘dabi’a ,idan kika rasa su kin zama fanko ba abin dayayi saura ya  allah ka ‘kara shiryar da mu akan sunana ..

kar kumanta kuyi comments da share wa post din mu jazakallahu khairan….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *