AREWA CELEBRITIES LABARAN DUNIYA

fim din india biyar dasuka fi karbuwa a idon duniya

Share

FINA FINAN INDIA TA BOLLYWOOD BIYAR DASUKA FI SHAHARA
babu shakka kampanin shirya fina finai ta india wanda aka fisani da bollywood sunyi suna a duniya gurin sako fina masu kyawu,daraja da kuma kawo kudi .masana sum kiyasta cewa kasar india,harkar film tana daya daga cikin abin dake kawo mata kudin shiga ..ko shakka babu wasu fim din sun fi wasu tsaruwa dama karbuwa gun al,umma,na farko a jerin su shine

  1.       DANGAL (AHALIN DAMBE) mahavir singh (amir khan ) tsohon dan kokawo ya gaza ciga burinsa na ciyo kambun zinare ,sanadiyar hani da maihinsa yayi masa cewar ya bar harkan kokawa yasami aiki da gwamnati yayi ,bin umurnin mahaifi yazama dole ,hakan yasa mahabir singh aje kokawa sai dai ya dauki alwashin cewa dan da zai haifa sai yaciwo maza kambun zinare,sai dai kash,mai dakinsa ‘ya’ya mata kawai take sambado masa ,’ya’ya mata har hudu ta haifo mai,hakan bai masa dadi ba,tunaninsa yaya maza, ne kadai zasu iya cika masa burinsa ,sai gashi wataran da yammaci makwabta sukayo sallama,sun kawo karar geeta da babita ,wai sun caskale wasu yara ,abin da yayi wa mahavir singh dadi ,bai maji hushin su ba,inda ya dauki aniyar koyar da su kokawa dun cikan burinsa ,cikin horarwa daya rika basu kuwa shine ,aske musu gashin kansu, kuma banda kula maza lols,banda cin nama ,da abinci mai nauyi hakan ko akayi yayin da geeta tayi nasarar ciwo kambun zinare ta duniya inda babita ta ciwo ta kasa
    randa aka saki fim din cinema 4,360 a haska fim din sannan fim din tayi nasarar samun kudi $100,000 dalal million amurkaahalin danbe nassblog.com

2.    SULTAN sultan ali khan (salman khan) mashahurin matashi dan kauyen haryana wanda ke rayuwa da babansa ,kakansa sai abokinsa govin ,arfa kyakkywar budurwa duk da cewa sultan matashi dan shekara talatin da yakiyin aure,zuwan ‘yar mai horaswa kauyen arfa kawai yaji yakamu da sonta ,kasancewa warta yar gidan kokawa hakan yasa da dauki alwashin sai dan kokawa zata aura,wannan yazam babban kalu bale ga sultan dan tabbbatarwa arfa irin son da yake mata ,yazo da,irar maihaifinta dan a koyamai dambe,arfa da sultan sunyi aure ,bayan samun nasararsu na zuwa cim kambun duniya ,nan arfa ta pahimci cewa tana da juna biyu,tsari da kuma dokokin dambe mai juna biyu bata zuwa,dawowar sultan daga kasar turkey ya tadda dan sa yamutu ,daman arfa tamasa kashedin zuwa yakiji…sultan yarasa dansa ,matar sa dalillin kokawa…a wata gefen ga aakash mai kampanin protect down ,kampaninsa taki karbuwa ,dan haka mahaifinsa yabashi sha warar inya naso kampanin sa ta karbu to dole sai ya nema dan kokawar gida ,bayan barin kokawa nawasu shekaru sultan dan soyyaya ya dawo da,ira …kokawa ita ta karbe mai mutuncin sa kuma ita zata dawo mai da ita….fim din ta fa tsaru…su meiyan cheng ,kubrah sait …wayafi burge ku a fim din….?
fim din sultan ta sami nasarori dama inda ta sami $96 million dala million din amurka a padin duniyasultan nassblog.com
3.      BAHUBALI. shivadu (prabhas )a wata masarauta a kasar indiya masarautar mishramati ,shivadu ya pada soyyayyada dawa ta dakariyar wata runduna,so dayake mata hakan yasaka shi hawa tsauni zuwa inda take ,,nan ya tsinci wata mask tata,doka da kokokin wannan runduna shi ne,batun soyayya ga dakariya babu,shiko shivadu yarika zuwa yana mata zanen pure masu bala,in kyau,,shugaban runduna yana ganin avantika ta fara soyyaya dan haka zatayi rauni gun abokan gaba ,,a wata masarautar ta mahishmati ,wata sarauniya ,sarauniya devesina a garkame ,bayan soyayya mai karfi ta kullu tsakanin shivadu da avantika shine ta fada mai kudirinta ita da  tawagarta gurin ceta sauraniya debesina.bayan sunyi nasarar ceto ta ,labari ya isa ga mugun sarki kattappa,,nan pa aka gwapza yakii..an kashe dala million $17 gun shirya fim din kuma sun sami dala million $98 ..kuma fin kadai cikin jerin wanda tazo da aga asalin telagu,wato kudancin india.bahubali nassblog

4.    PK (GASKIYA DAYA). tofa kun saba lamba alqur,an lols.itace fim din data zo na hudu cikin jerin fim din dasuka fi shahara suna da ma kawo kudi a kasar indiya,fim din ta fara ne da jaggu wacce taje karo karatu kasar belgium nan ta pada soyyayya da wani matashi dan asalin kasar pakistan safaraz yusuf ,soyyayya tai karpi suka shirya yin aure,kasan cewar mahaifinta mabiyin addinin hindu duk abin da zasuyi sai sun nemi tabara riki gun babban malamin su tapaswi,,shi ko pk daga wani duniyar yake, yawo ta kawo sa wannan duniyar ,nan wani mutumin kauye ya fisge masa masarrafin sa ,kuma saida wannan masararfin zai koma duniyarsu,shi mutumin kauyen zuwa yayi ya zaida wa tapaswi ,shi ko babban malami tapaswi cewa yayi ubangiji yace na gina majami,a nasanya wannan masarrafin,shiko pk yace tasa ce….nan gidan talabijin din su jaggu ta shirya mukabala tsakanin pk da malam tapaswi bam bam bole (lols)…inda pk yayi nasarar kure malam tapaswi mai sababbiyar lamba nan take suka kirawo opishin jakadan ci na pakistan domin kure mai karya,amsawar opshin jakadan cin pakistan keda wuya aka  ,sada safaraz yusuf da jaggu a waya….malam tapaswi ya ce! musulmai yan ta,adda ne,zai ci amanarta bayan su suka shirya komai…fim din ta sami nasarori da dama ciki har da wajen india pk gaskiya guda nassblog
namba na biyar kuma na karshe a wannan list itace

5.  3 IDIOTS ( DOLAYE UKU) ita wannan fim din dai tafara ne da shugaban makaranta wanda dalibai sukai wa lakabi da birus inda yake musu jawabin martabawa inda yake cewa ” rayuwa kamar kwai take kada kumanta duk shekara wannan makarantar tana samun masu neman gurbin shiga dubu dari uku dari biyu kawai ake debawa saboda haka kutana rayuwa tsere ce idan bakai sauri ba sambade ka za ayi .duk wanda yakalli fin dinnan bazai mance da farhan ba,raju rastogi mai gayya mai aiki ranchodas shamaldas chanchad (amir khan) sai kuma abokin gwabzawar sa catur salansa…inda catur ya kalubalanci abokan karatun nasa ranchodas ,cewa nan da shekaru goma a dawo ,aga waya fi samun nasara arayuwa,yana mai yiwa ranchodas dariya waishi sai dai yakare a malamin makaranta..”A is for apple,B is for ball” akarshe dai ranchodas shiya yi nasara dan ya zama kwararren injiniya ,catur ya fadi..fin din ta samu karbuwa sosai gun mutane ,inda tasami dalal million $57.05 million dalal amurka3 idiots nassblog
wanne kuka ga yafi dacewa yazam na farko?
ku fada mana ra,ayinku a comments box.

kobabu komai yaci ace

6.padvamati

7.ek tha tiger

8.barfi

9.rikon amana (bajrangi)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *