HAUSA LOVE STORIES

Danyar hukunci

Share

PARPAJIYAR KOTU.12 NOVEMBER 2025

nassblog/hausa love stories

bismillahi rahmanir  rahim, Sha biyu ga watan nuwanbar alip dubu da ashirin da biyar ,

sakataren kotu ya mike wannan kara itace mai lamba talatin 30 wanda kotu zata gabatar ayau sha biyun watan nuwambar dubu da ashirin da biyar,wannan case ta na tsakanin gwamnatin jaha ne da gwamnatin tarayya ,wadanda ake zarjin jalaludden mukhtar inkiya jal,hafsat yusuf ,rulwanu idris inkiya rilwan bisa aikata muggan laifuka biyar ,wanda ta kunshi ,pashi da makami,kisa ,sata,garkuwa da mutane hadi da ta’amuli da muggan kwayoyi,babban alkalin wannan jaha Dr.mallam mukhtar nakowa zai zartar da hukunci wa wadannan masu laifi.
sakataran kotu bayan yagama jawabin yamikawa alkali takardar daukaka kara,sannan ya zauna kujeransa…bayan judge alkali ya kare wa case file kallo na yan wasu dakiku,sannan ya kalle inda su jal,rilwan ,hafsat suke yace dasu “shin kun amsa tuhumar da ake mu”? guilty or not guilty.a tare suka furta not guilty (bama da laifi ) alkali yadanyi yan rubuce rubucensa sannan yaci gaba da cewa “shin ko lauya dake kariya na da abin cewa”
lauya mai kariya ya mike “sunana barrister khalid jibrin lauya mai kariya wa wadanda ake tuhuma ,ya mai girma mai shari,a zan fara da mai rokon kotu da ta yanke hukunci cikin jinkai da tausayi..idan mukayi lura wadanda nake karewa yara ne na manya dakuma sannan nun mutane iyayensu sunyiwa jaha hidima dama kasa baki daya wanda baza ataba mancewa da hakan ba ,abin da sukayi yana acikin xukatan mu ,muna cin moriyar hakan kuma insha allah yayan mu zasu taso suci gajiyar hakan ,duk abin da sukayi inmukayi duba da nazari ,zamu gane cewa kuruciya ce ke dibarsu wanda ina da yakinin cewa nan gaba zasu daina,kuma su zamto masu kishin kasa,fatan kotu mai alfarma zatayi duba wa al,amarin wannan yara ,nagode…”yakoma mazaunin sa
alkali yayi yan rubuce-rubucensa ;yadago yace” shin lauya mai tuhuma yana da abin fada”?lauya mai tuhumar wadanda ake xargi yamike “sunana barrister sani bello yana mai daga murya bansan wata irin canji lauya mai kariya yake nufi ba ,wadannan mutanen yana mai nuni da yatsa ,yayi murmushi pashi da makama ta,amuli da muggan kwawoyi manyan fa laifuka ake batu ba biredi suka sata ba,,mutanen dasukayi garkuwa da yar gwamna ,nan gaba ai yar shugaban kasa zasu su dauke matukar ba a dauki mataki kansu ba, ya mai girma mai shari,a barin irin masu wannan hali ciki al,umma ! ,zai jepa mutane cikin tsoro da fargaba,ina da tabbacin cewa kotu mai adalci zata zartar da hukunci kamar yadda kundin tsarin kasa ta tanadarwa masu irin wannan ta,asa…nagode’
jal,rilwan da hafsat suna murmusawa haba ai dad ne .. kotu tai tsit ana jiran hukuncin da alakali zai zartar.
alkali bayan yadan yi wasu yan rubuce rubuce yadago ya kalli al,umma yace”mun saurari bayanai daga bangarorin biyu,lauya mai kariya da lauya mai tuhuma danhaka kamar yadda kundin tsarin kasa da tanadar ,bayanai da hujjojin lauya…….wannan shi ne hukunci na…….

    mafaririn labari…

a wata yanki a jahar kaduna ,kabala ko kuce kabala kostin ,sanin kowa ne wannan yankin yanki ne na talakawa ,jabir da mahaifiyar sa  sai kuma kanwar sa  mahaifin nasu wanda mai ritaya ne ( retired civil servent)shekaru uku kenan bayan rasuwarsa ,jabir da mahaipiyarsu sun dogara ne da pension din dake zuwa musu duk wata da shio suke sha suyo sutura duk a ciki ,jabir ya gama hada ‘yan kwamatsan sa daya san zai bukata a jami’ar kaduna ta kaduna state university daya ke wata daki suka kama shi da wasu abokan sa su uku ,duk da cewa kabala kosting zuwa bakin gate din kasu bata da wani nisa sosai , hasali ma naira dari ce zata kawo ka har gate din kasu ,dalalinsa na kama gida shine kuwa yafison gida kusa da school,dan dayawa dalibai sukan taho makaranta da dare wasu ma har tdb sukeyi ma’ana till day break har sai gari ta waye.

jabir yace da ummansa, umma ki daina damin kanki akaina nifa ba yaro bane .dole man nada mu da akanku kaga fa daga kai sai kanwarka  kuka dai kawai kuka ragemun mahaifinku yatafi ya barmu,inka tafi inaso kamaida hankali gun karatunka ,bansan yawan abokai,haba umma kinga pa bakya da lafiya  ki rage yawan tunani,’yar lelen umma ki kula da umman mu kinji? kuma kitabba da da kullum tasha maganinta,yake fadawa kanwarsa ,’yar lele suke kiranata,to yaya,jabir yadauki jakarsa ,to ni natafi ‘yar llele muje kira kan ,fitar su ke dawuya suka sami wani mai adai dai  ta saho yace da shi ; degel 1 zaka kaini nawa zan bada yace dari hudu zaka bada yace dashi a,a sai dai fa ka biya three hundred ,kaima ai ka kwaso kaya…jabir yace dashi to babu komai.ingo nan yar lele yamikawa ‘yar kanwarsa naira dari biyu,jiki abinki kimaida  hankali wa islamiyya ,nan tayi tafiyar ta ,tafiyar  minta 9 ce ta kaisu degel 1 kasancewar ranar lahadi ce babu cinkoson hababen hawa.

   kaduna state university department of  computer science (h.o.d office)

alhaji mukhtar nakowa zaune office din head of department ta computer science a kujerar farko da aka tanada domin baki,jalaludden ne da abokinsa rilwan sunyi tsaye kowannen su yayi foldin din han dinsa

H.O.D dalilin daya sa muku kira woka alhaji shine ,su muke musanar dakai irin abin da ‘ya’yanka suke yi a wannan makarantar tamu yanzu haka department ta gaji da kore pe kore pen su,dan haka muka gayyato ka ,alhaji irin abin dasuke aikatawa yace ace tuni mun sallame su, ganin girmanka yasa muka daga musu kafa ,amman gasu inna musu karya su fada ma,..alhaji mukhtar yace nagode ,nagode h.o.d,zanyi musu magana insha allahu zasu daina ,nan  sukayi musa baha…h.o.d ya ce dashi you are welcome.ficewarsu ke da wuya alhaji mukhtar yace dasu maza ku jira ni cikin mota,soyake yakara faculty of biological science dan ganin wani amininsa  ,senior lecturer a department din,,,jal yace wa mahaifin nashi,dad kaje kurin zamu same ka gida …

          gidan alhaji mukhtar (malali kaduna)

bayan alhaji mukhtar yacigo gidansa tun tuni yana mai dakon dawowar dansa jalal,tun dazu dawowarsa sai  safa da marwa yakeyi,mai dakinsa kuma abin yadaure mata kai,yaya dai alhaji lafiya kuwa ka kasa tsaye ka kasa zaune ,ta jeho mai wannan tambayar?…

muhadu a kashi ta biyu….karkumanta kuyi share wa yan uwa da abokai…thank you! nogede, namaste wa masoya kallon zee world domin yanzu ba mata kadai ke kallon zeeworld ba,ina kuke matar wannan gida ,shin karya na fada? lols

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *