AREWA CELEBRITIES HAUSA LOVE STORIES

ahalin malunta

Share

wata rana wani aramma yana zaune da matarsa wata arammiya ,suna zaune cikin lumana da kwanciyar hankali,kwatsam sai aramma ya bijiro da batun kara aure.arammiya tace akamme? tofa kunjiya lols..aramma yace da ita ”Allah ne yace inkara ” arammiya tace ”infa kace Allah ne yace kakara kenan maganarka fa tana cikin Qur’ani”? aramma yace eh tana ciki ,arammiya tace to karanton ayar naji..kawai sai aramma ya kawo ayarda Allah madaukakin sarki yace idan kuntashi zakuyi aure to ku auri bibbiyu ko uku ko hudu: ”fankihu ma daba lakum minan nisa’i mathna wa thulatha war ba ‘a fa’in kiftun alla ta’adilu fa wahidatan”. sai arammiya tace ”to ai kai banda kai Allah ta’alah yace domin kuwa cewa yayi wadanda zasuyi adalci kai kuwa bazakayi adalci ba” aramma yace da matarsa wayace miki bazanyi adalci ba?

 

arammiya tace”llah ta’alah ne yafada” aramma yace to kenan maganar tana cikin qur’ani,arammiya kwarai kuwa tana ciki ,aramma yace to karantan ayar ,arammiya kuwa ta karanto mai ayar data ke cewa ”bazaku taba yin adalci ba tsakanin matayenku koda kuwa kunso yin hakan :walan tastadi’u an ta’adilu bainan nisa’i walau harastum”..dajin sauraron ayar aramma yayi dariya yace aike ce baka fahim cci ayar dakyau ba,arammiya tace to fahimtar dani man aramma!…..tofa akafta.

sai aramma yace ”ayar tana nufin baza kaji yanda kekeso da marya ba ,kuma hakane daidai irin son dakake wa uwargida ba,dole zaka fi son wata aciki.” arammiya tace a haka kafimci ayar? aramma yace ” kwarai ma da gaske” arammiya tace to kaje kayi aure Allah yasa adace.aramma yace amin…aiko haka akayi aramma sai yaje yayo aure yasake auro wata takwarararsu wato hafiza mai haddar qur’ani…dan ALLAH idan kaji/kinji dadin wannan kissar kuyi share wa ‘yan uwa da abokan arziki,da duk wata kafa ta sada zumunta da kuke ciki… nagode!

ina muke ma? lols ..bayan ango yagama shan amarcinsa da amarya harna tsawan sati guda ,rannan sai yakira uwargida dakin amarya dan yamusu nasiha da kuma rabon kwana,aramma yana fara jawabi kawai sai uwar gida tayi charap tace ”daya kenan”. aramma ya harare ta baice komai ba yacigaba da jawabinsa harya kammala.aramma yana kammala jawabinsa sai ya juya wajen amarya yace da ita ; ko kina da abun cewa ?nan ma uwar gida tace ”biyu kenan” aramma yace maye ina magana kina wani cewa daya daya biyu biyu? uwar gida tace ”yi hakuri aramma ina kirga rashin adalcin dakake yi ne tun yanzu”….aramma yace yanzu harna yi miki rashin adalci a zamannan? yayi mamaki , uwar gida tace eh ai daman tun farko nagaya maka bazakayi adalci ba,aramma yace da ita to gayamin rashin adalcin dana yi miki..tace nafarko yaune kagama kwanakinka adakin amarya ko? aramma yace eh! tace nida amarya wacece babba…aramma yace kece
tunda nice babban wannan zaman damukeyi adakin wa yakamata ayita?
aramma yace ”dakinki”
tace ”to yanzu a dakina muke”?
yace ”a,a”
sai tace to saurari na biyu”
jin hakan yasa aramma yayi wuf yace ”toh tunda hakane bari nayi adalci mu ko ma cikin qur’ani.uwargida kinyarda mu koma ? tace eh! kefa amarya kin yarda? amrya tace kwarai kuwa…aramma ya kallo su duk su biyun yace tsakaninku duk wacce takeda dalili acikin qur’ani sai tafara magana”
rupa bakinsa ke da wuya sai amarya ta daga hannu sama ,uwar gida ma haka ,aramma yace muna jinki uwar gida bamu dalili daga qur’ani, uwar gida tace ”wassabikunas sabiqunn” (ma’ana wadanda suka riga ku sune kan gaba) Allahu akbar su uwar gida manya…ko maye amarya zatace oho!
aramma yace kepa amarya meye taki dalilin? sai amarya tace ”walal akhiratu khairan wa abaqa” wato (ta karshe tafi maka alheri akan ta farko) nan fa aramma yajike da zufa ya rasa abin padi…can sai aramma yatashi a tsaye yace dasu ”duk kannin ku kuji tsoron Allah domin kuwa yana cewa :”qul innal awwaluna wal akhiruna lamajamu’una ila miqata yaumul ma’alum” ma’ana (kagaya musu dana farkon dana karshen tabbas zamu taraku a miqata ranar qiyamah)
yan’uwa masu hankali da tunani ,mu tashi mune mi ilimi domin tana da tasiri….
karkumanta …..nima aramma admin (lols )nace kuji tsoron Allah ku suburbuda mana comments tare da yin liking,dama share din post dinnan.

 

kafinan baran baku qissar wani bawan Allah mai tsoron Allah wanan mutumin ya shahara ana ganinsa a gidan mata masu zaman kansu da kuma guraren shan giya,har takai ga mutane suna masa kallon mutumin banza..sun masa mummunan zato kuma kyakkyawar karshe …harta kai ga mutane sukan tareshi ido da ido su ce dashi amma in ka mutu anya zaka sami mai maka sallah kuwa?

watara rana sarkin garin yaji kunci aranshi sai yakira daya acikin waziransa acikin duhun dare  cewa yazo ya zagaya dashi gari,dasshi batare da kowa yasan ko su waye ba ,haka suka sa kawayansu suka fita suka fara zazzagawa batare da wami yasan kosu suwaye ba ,babu mai ganewa ma sarki ne,kwatsam sai suka cikaro da gawa ahanya ,kowa yana ta abin daya dameshi ,saboda sunaga wulakkantacecn mutumin nan ne ,sai sarki yayi wa mutanen garin magana ya bakuga mutun akwance kamar yamutu ba sai duk suka amsa ai wannan mutumin kaza da kaza ,kowa yana furta abin da tazo daga bakinsa ,sai sarki yace duk da haka dai baza abar gawa hakan an a kwance ba,a dauke shi akaishi gidansa ,ana ina gidansa matar sa ta ganshi yamutu sai ta pashe da kuka  tana cewa Allah yajikanka mijina mai tsoron Allah waliyin allah mai kiyamul laili ami kaza mai kaza ,kan mutane sai yabi ya kulle ,sai sarki yace da ita aipa ga abin da mutane suke fada akan mijinta ,kuma kina fadin wani abu daban ,tace eh kwarai kuw a mijina  yakance yakanbi kowani wurin shan giya agarinnan yasiye giyan yataho gida ya zubar yace akalla yau na kubutar da musulmai daga padawa sabon allah da apkawa haramun,mijina yakanje gidan mata masu zaman kansu yabi daki daki yatanbiyi kowacce kudin datake bukata  aranar yabata da sharadin baza tayi zina da kowa ba ,idan yadawo gida saiyace nagodewa allah akalla na kubutar da al’umnma musulmai aukuwa zinace zinace a wannan rana ,mutane da suka ji haka duk sai jikin su tayi sanyi ,suka jinjinawa kokarin wannan bawan allahn….sun masa munmunar fahimta shikuma yayi kyakkyawar karshe….

zamu cigaba…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *